Gwamnan Kano ya roƙi da a rage farashin kujerar Hajjin bana
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya roƙi Gwamnatin Tarayya da ta duba yiwuwar rage farashin kujerar Hajjin 2025 saboda matsalolin tattalin arziki da ƙasar ke fuskanta a halin yanzu.
Gwamna Yusuf ya yi wannan roƙon ne a taron da Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta shirya don ƙaddamar da shirin mayar da rarar kuɗi, Naira miliyan 375 ga mahajjatan Kano da su ka halarci Hajjin 2023.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, an mayar da kuɗin ne saboda wasu hidimmomi ds su ka biya, amma ba a samu damar aiwatar da su ba a lokacin aikin Hajjin 2023.
Gwamna Yusuf ya nuna godiyarsa ga gwamnatin Saudiyya bisa ƙwazon da ta nuna wajen mayar da kuɗin cikin gaggawa da tausayi.
Haka nan ya yaba wa Hukumar Kula da Hajji ta Ƙasa (NAHCON) kan kulawar da suka nuna da kuma gaggawar da aka yi wajen kammala aikin mayar da kuɗin.
A nashi ɓangaren, Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Laminu Rabiu Danbaffa, ya bayyana cewa an mayar da jimillar Naira miliyan 375 zuwa jihar don rabawa mahajjatan da suka halarci Hajjin 2023.