Gwamnatin Taraiya ta dakatar da kamfanin jiragen Max Air sakamakon haɗari a Kano

  Gwamnatin Tarayya, ƙarƙashin Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Ƙasa (NCAA), ta sanar da dakatar da ayyukan kamfanin Max Air biyo bayan wani haɗari da ya faru a daren jiya Talata a filin jirgin sama a Kano.

Wani jirgin saman Max Air B734 mai lamba 5N-MBD, ya gamu da fashewar taya a filin jirgin saman Malam Aminu Kano, Kano a jiya Talata, 28 ga watan Janairu, 2025 da misalin karfe kisan 11 na dare.

Wannan shi ne karo na uku cikin watanni uku da jirgin Max Air ke yin haɗari.

Duk da cewa an kwashe fasinjoji 53 da ke cikin jirgin ba tare da jin rauni ba, an rufe jirgin na wani dan lokaci kafin hukumar kula da filayen jiragen sama ta ƙasa (FAAN) ta bude titin jirgin da karfe 8:00 na safiyar yau Laraba.

"Sakamakon wannan lamari, an rufe aiyukan kamfanin Max Air na tsawon watanni uku da za ta fara daga tsakar dare, 31 ga watan Janairu, 2025, don ba da damar tantance ayyukansa a cikin gida daga mahukuntan hukumar NCCA," in ji sanarwar daga NCAA.


Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org