Har yanzu Nijeriya na ganin illar kashe Sardauna, in ji Shehu Sani
Tsohon Sanatan da ya wakilci Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya ce kisan gillar da aka yi wa tsohon Firimiya na Arewacin Najeriya, Sir Ahmadu Bello, har yanzu yana damun kasar.
An kashe Sardaunan Sokoto, Sir Ahmadu Bello, a ranar 15 ga Janairu, 1966, lokacin juyin mulkin soja na farko wanda wasu manyan sojoji ‘yan kabilar Igbo su ka jagoranta.
A cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Shehu Sani ya ce wadanda su ka aikata wannan abin sun shuka tsiron sharri a cikin kasar.
Yayin da ya ke yabawa halin kaskantar da kai da kuma rayuwar kamun kai na tsohon jagoran Arewacin, Sani ya ce ya sadaukar da komai don al’ummarsa da kasarsa, amma ya mutu talaka marar wani abu na more rayuwa.
A cewarsa, Sardauna ba shi da gida, mota, ko kamfani da aka danganta da shi ko wani daga cikin ‘yan uwansa a Kaduna.
“Ga mu da muke zaune a Kaduna, inda Marigayi Firimiya na Arewacin Najeriya ya rayu, ya shugabanta, kuma aka kashe shi cikin zalunci, ba mu iya gano wani gida, mota, ko kamfani da aka danganta da sunansa ko na wani daga cikin iyalansa ba.
“Bayan an kashe shi, an dauki dukiyarsa zuwa gidansu na iyali a Sokoto. Marigayi Sardauna ya sadaukar da komai don mutanensa da kasarsa, amma ya mutu talaka marar wani abu na more rayuwa."
Alfijr News