HARAJI: "Ashe a baibai aka baiwa ƴan Arewa bayanan dokar haraji, sai yanzu muka gane gaskiya - Inji Gwamnan Nassarawa
Engr. Abdullahi Sule, gwamnan jihar Nasarawa, ya ce an yaudari ƴan Arewa da cewa kudirin sake fasalin haraji zai haifar da karin nauyin kudi da matsin tattalin arziki a ƙasar.
Kalaman Sule na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta goyi bayan kudurin dokar harajin da ke gaban majalisar dokokin kasar.
Da ya ke magana a wani shiri a gidan Talabijin na Channels a jiya Alhamis, Sule ya ce NGF ta amince da sake fasalin haraji da nufin kawar da wasu kura-kurai da kuma samar da tsarin biyan haraji mai sauki ga talakawa.
Sule ya kuma kawar da ra’ayin da ke nuna cewa an samu baraka tsakanin gwamnonin Arewa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
“Yawancin mutanen arewa an sayar musu da ra’ayin cewa za a kara haraji. A yau, ta wannan yarjejeniya, babu ƙarin haraji," in ji shi.