Hukumar EFCC da ke yaki da cin hanci a Nijeriya ta kori jami’anta 27 bisa laifin zamba da rashin da’a
Hukumar EFCC Ta Kore Ma’aikata 27 Saboda Laifukan Zamba da Rashin Da’a
A wata sanarwa da Dele Oyewale, Shugaban Sashen Watsa Labarai na EFCC, ya fitar, ya bayyana cewa:
“Don tabbatar da gaskiya da kawar da munanan halaye daga cikin hukumar, Hukumar Yaki da Rashawa da Zamba ta Kasa (EFCC) ta sallami ma’aikata ashirin da bakwai (27) daga aikinsu a shekarar 2024.
“An sallami ma’aikatan ne Saboda aikata laifuka daban-daban da suka shafi zamba da rashin da’a. Sallamar tasu ta biyo bayan shawarwarin Kwamitin Ladabtar da Ma’aikata na EFCC, sannan aka tabbatar da matakin a karkashin jagorancin Shugaban Hukumar, Mista Ola Olukoyede.
“Olukoyede ya sake jaddada kudurin hukumar na rashin sassauci ga cin hanci da rashawa, yana mai gargadin cewa babu wani ma’aikaci da ya ke da kariya daga ladabtarwa. Duk wata zargin da aka yi wa wani ma’aikaci za a bincike shi kwata-kwata, ciki har da batun zargin dala dubu $400,000 da ake yadawa kan wani shugaban reshe da ake tunanin yana cikin ma’aikatan hukumar. Dokokin hukumar suna nan daram kuma za a ci gaba da mutunta su a kowane lokaci.
“Haka zalika, hukumar na sanar da jama’a kan wasu bata-gari masu kiran kansu jami’an EFCC don damfara da sunan Shugaban Hukumar.
“An gurfanar da wasu mutane biyu da ake zargi, Ojobo Joshua da Aliyu Hashim, a gaban Mai Shari’a Jude Onwuebuzie na Babbar Kotun Birnin Tarayya, Abuja, bisa zargin tuntubar tsohon Manajan Daraktan Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya, Mista Mohammed Bello-Kaka, suna neman dala miliyan $1 daga gare shi don yin ‘sulhu’ a binciken karya. Irin wadannan mutane na nan suna neman wadanda za su yaudara.
“Olukoyede mutum ne mai gaskiya wanda ba zai lamunci tasirin kudi ba. Jama’a na da shawarar kawo rahoto kan irin wadannan mutane marasa mutunci ga hukumar.
“Bugu da kari, hukumar ta samu labarin yunkurin bata suna da ake shiryawa domin kaiwa kan wasu ma’aikata. Wadanda ake bincika kan wasu laifukan tattalin arziki da kudi, wadanda suka kasa yin tasiri kan masu bincikensu, sukan nemi yin amfani da dabarun bata suna. Ana rokon jama’a kada su kula da irin wadannan mutane.”