Huukumar Yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, ta sake gurfanar da tsohon Ministan wutar lantarki, Sale Mamman don sake nazari akan hanyoyin da aka kashe kudaden

 Bayan Shari'ar Faransa dake Gudana a kasar Faris, hukumar Yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, ta sake gurfanar da tsohon Ministan wutar lantarki, Sale Mamman don sake nazari akan hanyoyin da aka kashe kudaden wutar lantarki na lokacin  Gwamnatin Buhari. 

Shari’ar tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, ta ci gaba a ranar Laraba, 22 ga Janairu, 2025, a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, karkashin jagorancin Mai Shari’a James Omotosho, inda Hukumar EFCC ta gabatar da shaida na takwas (PW8).

Shaidar, Abdullahi Suleman, wanda yake mai canjin kuɗi ne, ya bayyana yadda aka yi zargin fitar da fiye da Naira biliyan 22 daga Ma’aikatar Wutar Lantarki lokacin da Mamman yake Minista. Ya ce kudaden da aka karɓa sun kasance naira, amma an mayar da su dala ta asusun kasuwancinsa.

EFCC na tuhumar Mamman da laifuka 12 da suka shafi haɗa kai don yin almundahana ta hanyar wanke kuɗi da yawansu ya kai N33,804,830,503.73.

A zaman kotun na ranar Laraba, Suleiman ya bayyana yadda wasu asusunsa guda 12 suka karɓi kuɗaɗe daga Ma’aikatar Wutar Lantarki ba tare da yin wani aiki, kwangila ko ayyuka ba. Kamfaninsa da suka haɗa da Prymint Investment Limited, Strong Field International Projects Limited, Mintedge Nigeria Limited, da sauransu, aka yi amfani da su wajen mu’amalolin kuɗi.

Ya ce: “Na san Alhaji Maina Goje, muna aiki iri ɗaya. A wani lokaci a shekarar 2019, Maina ya nemi in ba shi lambobin asusun bankina don gudanar da mu’amala, sai na ba shi. Ya fara tura kuɗi, ni kuma na mayar masa da su cikin dala. Ya cigaba da neman karin asusu, yana gaya min abin da zan yi da mu’amalolin.”

Suleman ya ƙara da cewa daga kiyasin da ya yi, ya karɓi fiye da Naira biliyan 22 daga mu’amalolin. Ya kuma bayyana yadda wani mutum da ake kira Musbhu, wanda suka kira "Yaro Minister" saboda yana aiki tare da Saleh Mamman, ke zuwa wajen sa da umarnin abin da za a yi.

Lokacin da aka nuna masa wasu takardu (Exhibit X), waɗanda suka nuna bayanan mu’amalolin kuɗi a asusunsa, ya tabbatar da cewa su ne asusun da ya baiwa Maina Goje.

Babban mai gabatar da kara, Rotimi Oyedepo, SAN, ya gabatar da wasu shaidu daga FCMB da suka haɗa da bayanan asusu da aka tattara a wata wasika da aka rubuta wa EFCC a ranar 16 ga Agusta, 2024, wanda aka karɓa a matsayin hujja.


Mai shari’a James Omotosho ya dage sauraron karar zuwa ranar 23 ga Janairu, 2025, domin ci gaba da shari’a.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org