IN DA RANKA: Yadda wani Matashi ya dirƙawa wata aljana ciki bisa rashin sanin ita ba bil Adama ba ce a ƙauyen kaɗaki dake ƙaramar hukumar Giwa Jihar Kaduna....
Sai dai lamarin ya zo da rikitar wa, sakamakon yadda makusantar matashin mai suna Habibu Musa da akafi sani da (Bota) suna bayyanama wakilan Jaridar ALFIJIR NEWS cewa! sukan haɗune a wata kasuwa da take ciki duk bayan mako guda ta Galadimawa a sifar bil'adama ɗin, inda daga nanne suka haɗu har suka saba da juna soyayya ya ƙullu.
Wakilan rukunin Kamfanin dillancin Labarai ta ALFIJIR HAUSA NEWS LTD sun ci gaba da bin diddigin lamarin, har sai da suka samu zantawa da ɗaya daga cikin abokanan Matashi Habib (Bota) da a halin yanzu yana kwance rai ga hannun Allah mai suna Minka'iku ( Kowa Naka) ya bayyana ma wakilan mu cewa! suna keɓewane idan zasuyi fira da juna, yadda wani abokinsu yake taimaka masu da Ɗakinsa na kwana toh a zarginsa a nanne dai al'amarin ya faru.
Matashin wato saurayin Aljanan Habib (Bota) dai yana cikin mawuyacin hali, sakamakon kamasa da wananan aljanar tayi kuma take bayyana tabbacin sai ta ga bayansa, ko kuma ya aure ta ya samu zaman lafiya, saboda a irin jiyo junansu da sukeyi turmi da taɓarya an samu shigar CIki inda a halin yanzu Aljanar mai suna Mero take ɗauke da juna biyu kamar yadda take bayyana haka a jikin saurayin nata.
Alfijr News
#BMW
#newyear
#newyears