Jami'an tsaro sun yi nasarar hallaka ƙasurguman ƴan ta'addar daji a jihar Zamfara

 Kimanin manyan ƴan ta'adar daji Ukku ne jami'an tsaro suka halaka su a jihar Zamfara yayin wani artabu da Jami'an tsaro.

Waɗanda harin ya rutsa dasu sun haɗa da Kachallah  Mai Shadda, Kachalla Gurgu, da Kachalla Mai Dadawere dukkanin su dai sun gamu da ajalin su kusa da ƙauyen Gangara yayin da suke ƙoƙarin gudu bayan da suka ji ruwan wuta daga hannun Jami'an tsaron.


Bisa ƙiyasi dai ana zargin an halaka Ƴan ta'addar dajin kimanin guda Sittin a cewar zagazola makama, kazalika yanzu haka manyan ƴan ta'adar daji guda Biyu da sukayi ficce Ado Aleru da Bello Turji suna ta rayukan su saboda ruwan wuta da ake a dazukan Shinkafi da Maradun na jihar ta Zamfara.


Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org