Kaddara! Saurayinta Ya Mutu A Otel Lokacin Da Ta Ziyarce Shi Ya Bata Iphone 16
"Dazu da safe, Manajan gidan hotel na Palasa dake yankin Gwagwalada Abuja ya kai kara ofishin 'yan sanda na Gwagwalada bayan wani mutum ya mutu a dakin hotel din da ya kama shi da budurwar tasa.
"Sunan wanda ya mutu Lawal Ibrahim, sunan budurwar tasa kuma Maryam Abba daga birnin Dutsen Jihar Jigawa, wanda sun hadu a social media watanni uku da suka wuce.
"Abinda ya faru shine, Lawal ya kira Maryam zuwa Abuja, jiya da dare ya sauke ta a Palasa Hotel suka yi abinda za su yi, da garin yau Laraba ya waye da misalin karfe 6 na safe suka sake yi, Maryam ta ce suna cikin bàďàĺàr nè ya fado daga ķanța ya suma numfashinsa ya dauke, ta yayyafa masa ruwa bai farfado ba.
"Shine sai ta sanar da ma'aikatan gidan hotel din akazo aka daukeshi aka kai asibiti inda Likita ya tabbatar da Lawal Ibrahim ya mutu.
"A yanzu haka Maryam tana hannun 'yan sanda an kaita zuwa Force CID Abuja don tabbatar da bincike akan musabbabin mutuwar abokin mutumin, abubuwa da aka samu sun hada da kankana da miyagun kwayoyi masu kara ķaŕfin jìmà'ì.
Darasin da zamu dauka anan shine:
👇
Maryam 'yar Jihar Jigawa ne daga birnin Dutse, ta yi wa iyayenta karya ta taho Abuja domin a yi laĺàțà da ita, abokin ĺàĺațaŕ ya mutu a kanta lokacin da suke cikin yin fàšìkanci, Allah ne kadai Ýa san ranar da za ta kubuta daga wannan tuhuma na kisan kai da ake mata.
"Mutane mu ji tsoron Allah, babu wanda ya san a wani irin yanayi ajali zai zo masa, tabbas akwai abin takaici ace mutum musulmi yayi mummunan karshe irin wannan
"Matansa da 'ya'yansa da iyayensa, da 'yan uwa da abokansa duk sai sun yi da na sanin saninsa a rayuwa.
"Haka ita ma yanzu Maryam sai ta yi nadamar zuwanta duniya, domin yanzu lissafi ya kwabe mata, iyayen ta da 'yan uwanta da sauran samarinta da take yaudara duk za su san halin da take ciki
"Don Allah mu yi iya bakin kokarinmu wajen aikata ayyukan alheri tare da gudun munanan abubuwa da zasu rusa mana tarihi su zubar da kima da mutuncin mu
"Allah Ya tsare mana imanin mu, Ya bamu karfin yakar shaidan
Shi kuma Lawal Ibrahim Allah Ya yafe masa, Ya bashi Aljannah don rahamar Sa."
Daga Ďațti Asśalafìy