Kano: Ana zargjn wani babban jami'i da "wawure" kuɗaɗe a REMASAB

 Wata ƙungiya mai suna Abba ba Butulu Bane ta yi kira ga Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da ya sanya a yi bincike a Hukumar Kwashe Shara ta JIHAR Kano, REMASAB bisa zargin wani babban jami'i da "wawure" kuɗaɗe a hukumar.

Hakazalika ƙungiyar, a wata sanarwa da jami'in ta na hulda da jama'a, Mukhtar Gwammaja ya fitar a yau Laraba a Kano, wacce ya aikewa Daily Nigerian Hausa, ta yi kira ga shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar, Muhuyi Magaji Rimin-Gado da shi ma ya kama tare da tuhumar jami'in.


Sanarwar ta ce shugaban ƙungiyar, Abdullahi Inuwa Grima, ya yi zargin cewa jami'in na karkatar da wasu kuɗaɗe da ya kamata a ce an saka su a asusun gwamnati.


Girma ya yi zargin cewa jami'in na sama da fadin kudin gwamnati ne sakamakon wani gajeren hutu da Shugaban hukumar, Ahmadu Haruna Danzango ya yi sakamakon rashin lafiya, inda ya kara da cewa "hakan ya sa ake kallon hakan ya baiwa wani jami'in hukumar damar sama da fadi da wasu kudade a hukumar". 


"Hakan yasa mu ke kira ga Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da ya kafa kwamitin bincike domin gano wannan badakalar kudaden da ake yi a hukumar ta REMASAB.


"Haka shi ma shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da ya bincika wannan zargi ya kuma hukunta wanda ake zargi idan ya tabbatar da zargin," in ji sanarwar.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org