Kashi 60 cikin 100 za a ƙara a farashin kiran waya - Gwamnatin Taraiya

 Ministan sadarwa da kirkire-kirkire da tattalin arziki a fannin fasaha, Bosun Tijani, ya bayyana cewa karin kudin kira da ke gabatowa ba zai wuce kashi 60 cikin dari ba.


A tuna cewa kamfanonin sadarwa a kasar sun yi ta kira akan karin harajin kashi dari na kuɗaɗen kiran waya da data saboda hauhawar farashin kayayyaki da faduwar darajar Naira da sauransu ya yi musu illa sosai.

Amma da ya ke magana yayin wata hira da gidan Talabijin na Channels TV,  Tijani ya ce gwamnati ta amince cewa an kara kudin kira a fannin sadarwa.

Sai dai ya ce gwamnati ba za ta iya ƙara kashi 100 cikin 100 da kamfanonin ke bukata ba.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org