Ku ƙara hakuri cikin shekarar nan farashin kayan masarufi zai sakko- gwamnatin taraiya ga ƴan Nijeriya

 Ministan kuɗi na Najeriya, Wale Edun, ya buƙaci ƴan kasar su bai wa gwamnati lokaci, kasancewar tsadar rayuwa da ake fama da shi a ƙasar zai sauko nan ba da dadewa ba.

A hirarsa da BBC, Mista Edun ya ce ya yi amannar cewa hauhawar farashin kayayyaki da a yanzu ta kai kashi 35% za ta ragu da rabi cikin shekarar nan.

Ya alaƙanta matsalar tattalin arziƙin da ƙasar ke fuskanta kan gyare-gyaren harkokin kuɗi da gwamnati ta yi a baya-bayan nan, sai dai ya yi imanin cewa ƴan ƙasar za su ga amfanin hakan nan ba da jimawa ba.

Ƙwararru a fannin tattalin arziƙi sun alaƙanta hauhawar farashin kayyyakin kan karyewar darajar ƙudin ƙasar, da cire tallafin man fetir da kuma matuƙar buƙatar kayyayaki a lokacin bukukuwan ƙarshen shekara.

@Daily Nigeria Hausa 

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org