Mutune 16, ciki har da ƴan bijilanti sun mutu a harin sama na soji a Zamfara
Akalla mutane16 ake fargabar sun rasa rayukansu bayan wani harin sama da sojoji suka kai a garin Tungar Kara, karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.
Jaridar TheCable ta samo rahoto daga Zagazola Makama, wani masani mai kawo rahotanni kan yaki da ta'addanci a yankin tafkin Chadi, cewa majiyoyin sirri sun bayyana cewa wadanda abin ya shafa sun hada da mambobin Kungiyar Tsaro ta Al’umma ta Zamfara (ZCPG), ƴan sa kai, da mazauna yankin da aka kira don tunkarar harin da ‘yan bindiga suka kai.
“Sojojin sun zaci ƴan bijilanti din su ne yan bindigars, bayan yan bindigan sun tsere daga wurin,” in ji rahoton.
“a halin yanzu an gano gawarwaki 16, amma adadin wadanda suka mutu baki daya bai bayyana ba.”
Olusola Akinboyewa, daraktan hulda da jama’a da labarai na hedkwatar Sojojin Sama na Najeriya (NAF), bai maida martani kan tambayoyin TheCable game da lamarin ba.