Na kwashe shekaru ashirin ina fim a Amurka amma har yanzu a talauce na ke - Djimon Hounsou
Shahararren jarumin Hollywood din nan Djimon Hounsou ya bayyana cewa ya na ci gaba da fuskantar matsin tattalin arziki duk da sana'ar fim da ya ke yi sama da shekaru ashirin.
A wata hira da CNN a wani shirin su na matasan Afirka, a yau Asabar, Hounsou ya bayyana cewa ya na ganin cewa ana yi masa ƙwange a albashi kuma har yanzu ya na fama da talauci.
"Har yanzu ina fama yanayi a rayuwa. Na kasance cikin harkar shirya fina-finai sama da shekaru ashirin, tare da lashe lambobin girma na Oscar guda biyu da fina-finai da yawa, amma duk da haka, har yanzu ina fama da rashin kuɗi. Babu shakka ƙwangen albashi ake yi min," inji shi.
Wannan tonon silili ya ba wa mutane da yawa mamaki, ganin irin nasarorin da ya samu, gami da lashe lambar yabo ta Academy sakamakon kwazon saba fim din 'Blood Diamond' da 'In America'.