Na tanadi ƙwararan hujjoji da zan fasa ƙwai kwananan - Baffa Bichi

 Korarren Sakataren Gwamnatin Kano, SSG, Dakta Baffa Bichi ya ce yana da ajuyayyun ƙwararan hujjoji a kan gwamna Abba Kabir Yusuf da Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso da zai fito da su nan gaba kaɗan.

Wannan shi ne karo na farko da Bichi ya yi magana tun bayan cire da gwamnan Kano ya yi a matsayin sakataren gwamnati.

Da ya ke magana ga magoya bayan sa a juya Alhamis bayan ya dawo daga Umrah, Bichi ya ci alwashin tona asiri, inda ya ce ya na da hujjoji da shaidu na badaƙala da a ka yi a gwamnati.

"Na gode Allah na gama lafiya. Wannan ba lokacin magana ba ne amma ina da hujjoji ƙwarara da zan fasa ƙwai. Zan tona asiri don mutane su san ko su wadanne irin mutane ne.

"Maciya amana ne kuma butulaye ne. Mun taimaka musu amma sun mana butulci amma ba komai, za mu tona musu asiri," in ji Bichi, da ake ganin da Abba da Kwankwaso ya ke.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org