Rundunar ‘yan sanda ta Bauchi ta kama mutum biyu bisa zargin yin luw@di da kananan yara a wurare daban-daban.

 A Tilden Fulani, an kama Aminu Musa, mai shekaru 41, bisa zargin yin luw@di da yaro mai shekaru 11, inda ya yaudarashi da kudi da abinci. 

Haka zalika, a cikin garin Bauchi, an kama wani Adamu Abdullahi, mai shekaru 38, da zargin tilasta wa yaro mai shekaru 10 shiga gini ba a kammala ba, tare da aikata wannan mummunan abu. Dukkan wadanda ake zargin sun amsa laifinsu.

Haka kuma, rundunar ta cafke wasu mutum biyu, Abubakar Yakubu da Almustapha Hassan, bisa zargin mallakar bindigu na gida da kuma shiga aikin fashi da makami. 

An samu bindigu biyu, mashina biyu, adda, da wasu kayayyaki daga hannunsu. 

Sun amsa laifinsu tare da bayyana yadda suke fasa mashina da kayayyaki su sayar. 

Rundunar ta yi kira ga al’umma su ci gaba da bayar da hadin kai da rahoton duk wani motsi da basu amince da shi na ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org