SHEKARAR SA 10 YANA DANSANDA BOGI A KADUNA

Hukumar Yan'sanda ta kasa reshen Jihar Kaduna ta kama Wani mutum Dan kimanin shekaru 40 daya kwashe tsawon shekaru 10 yana aikin Dansanda a jihar.

Mutum Mai suna Rabiu yana karbar kes kuma yana zuwa Kotu don jin bahasin kararraki duk a cikin basaja.


Yansanda sun kama shi ne bayan daya kasa amsa musu wasu tambayoyin inkiya da su Yan'sanda me suke yiwa kan su, kuma sun kama shi da I.D Card da wasu kayayyakin amfanin Yan'sanda.

Jami'in Hulda da jama'a na rundunar Yan'sanda ta kasa reshen Jihar Kaduna DSP Mansoor Hassan ya ce akwai irin su da yawa, ya ce zasu gudanar da bincike a kan shi idan suka kammala zasu Mika shi gaban Kotu.

KHM TV

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org