Shugaba Tinubu ya dauki sabbin alkawura a wannan sabuwar shekarar
Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya yi fatan alheri game da makomar kasar nan a wannan sabuwar shekara ta 2025 a bana, inda ya ƙarfafawa ’yan Nijeriya gwiwa su ci gaba da kasancewa masu haɗin kai.
A cikin saƙon sabuwar shekarar da ya aike, shugaban ya tabbatarwa al’umma cewa, sadaukarwarsu a wata 19 da suka gabata, ba za ta tafi a banza ba.
Ya ce ya yarda al’umma sun fuskanci matsaloli a bara, amma ya bayyana tabbacin ganin sabuwar shekarar za ta kawo sauye-sauye masu kyau, inda ya yi hasashen raguwar farashin man fetur, da ƙara ƙarfin ajiyar ƙasa, da haɓakar ciniki da zuba jari.
Sai dai har yanzu shugaba Tinubu ya ce, ƙarin farashin abinci da kayayyakin more rayuwa na ci gaba da zama babbar matsala.
Ya kuma bayyana shirin ƙirƙirar kamfanin kula da lamuni na kasa, da zai taimaka wajen ba ’yan kasuwa damar samun rance, tare da bukatar ’yan Nijeriya su mayar da hankali wajen haɗin kai, da aiki tare domin gina ƙasa mai albarka.