Shugaban Amurka , Donald Trump ya ba da umarnin kai samame a makarantu, coci-coci da asibitoci
Shugaban Amurka , Donald Trump ya ba da umarnin kai samame a makarantu, coci-coci da asibitoci domin tilasta kamen bakin haure a ƙasar.
Wannan doka, wacce take daya cikin dokoki sama da 100 da ya sanya wa hannu, ta haifar da fargaba a Najeriya da sauran kasashen duniya.
Trump ya bai wa hukumomin shige da fice na Amurka ikon kama mutanen da abin ya shafa a wani mataki da ya zama akasin dokar da a baya ta maida wuraren su zama amintattu ga baƙi.