Trump ya dakatar da bada tallafi ga ƙasashen waje

 Amurka ta dakatar da ba wa kasashen waje tallafi nan take kamar yadda wata takardar gwamnati da ke kunshe da umarnin wadda aka yi satar fitar da ita ta nuna.

Sai dai dakatarwar ba ta shafi bayar da taimakon abinci da bayar da kudade ga harkokin sojin Isra'ila da Masar ba, kamar yadda takardar wadda BBC ta tabbatar da ita ta nuna.

Ma'aikatar harkokin waje ta Amurkar ce ta bayar da umarnin ga jami'ai da ofisoshin jakadancin kasar na waje.

Matakin ya biyo bayan umarnin da Shugaba Trump ya bayar ne a ranar Litinin na dakatar da bayar da tallafin raya kasashen waje tsawon kwana 90, har zuwa lokacin da za a sake duba tsarin ta yadda zai dace da manufofinsa na kasashen waje.

Amurka ita ce babbar wadda ta fi ba wa kasashen duniya tallafi inda ta kashe dala biliyan 68 a 2023, kamar yadda alkaluman hukuma suka nuna.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org