Wutar dajin Los Angeles ta haddasa asarar dala biliyan 150 a California

 Wasu alƙaluman ƙwararru da ke sanya idanu kan wutar dajin Los Angeles can a jihar California ta Amurka sun nuna yadda adadin ɓarnar da wutar ta haifar kawo yanzu ya iya zarta dala biliyan 150, ninki 3 na asarar da a farko aka yi hasashen wutar za ta haddasa.

Wutar dajin ta fiye da mako guda wadda a baya masana su ka ƙiyasin za ta haddasa asarar dala biliyan 50, tuni suka sauya matsaya inda ƙwararrun ke cewa tun a yanzu wutar dajin ta haddasa asarar da ka iya zarta dala biliyan 150 a wani yanayi da har yanzun ba a iya shawo kanta ba, lura da yadda ƙaƙƙarfar iskar Santa Ana da ke rarraba wutar zuwa sassa daban-daban ke barazana ga ƙoƙarin da ake na kashe wutar.


Masu aikin kashe gobarar sun bayyana cewa zai iya kai aƙalla kwanaki 3 a nan gaba gabanin iya shawo kan wutar lura da yadda iskar ke mayar da aikinsu baya.


Zuwa yanzu wutar dajin ta hallaka mutane 24 baya ga ƙone kadada dubu 40 a iya yankunan birnin na Los Angeles yayinda ta ƙone kadada dubu 23 a Palisades a wani yanayi da kuma wutar ke barazana ga Brentwood da Encino da kuma Westwood.


A gefe guda mahukuntan na Los Angeles sun ce zuwa yanzu wutar ta ƙone gine-ginen da suka kai dubu 12 da 300, a wani yanayi da aka kwashe mutanen da yawansu ya kai dubu 92 ake kuma kan hanyar kwashe wasu ƙarin dubu 89.

Ƙwararru a ɓangaren kiwon lafiya na ci gaba da kiraye-kiraye wajen ganin al’ummomin da ke kusa da yankunan da wannan wuta ke ci gaba da ci kan su kaucewa shaƙar hayaƙinta saboda illar hakan ga lafiya.

Tuni da aka samar da asusun tallafawa waɗanda wannan ibtila’i ya shafa, galibinsu waɗanda suka rasa muhallansu da dukkanin abin da suka mallaka.


.Rfi

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org