Wutar lantarkin fadar shugaban kasa da wasu yankuna ta ɗauke sakamakon sace wayar wutar
An samu katsewar wutar lantarki a wasu sassa na Fadar Shugaban Kasa da Maitama, Wuse, Jabi, Lifecamp, Asokoro, Utako, da Mabushi.
Hakan ya biyo bayan barnar da aka yi wa layin wutar 132kV da kuma sace wayar wuta ta karkashin kasa da ke ba da wutar lantarki mai yawa zuwa tashar wutar lantarki ta Katampe a tsakiyar birni.
Batagarin sun kuma sace wani kebul mai tsawon mita 40.
“Saboda haka, yankunan da suka fuskanci katsewar wutar lantarki sun hada da Maitama, Wuse, Jabi, Life Camp, Asokoro, Utako, Mabushi, da kuma wasu sassan Fadar Shugaban Kasa,” in ji Babban Manajan Hulda da Jama’a na Kamfanin Wutar Lantarki na Najeriya (TCN), Ndidi Mbah, a cikin wata sanarwa ranar Juma’a.
Mbah ta bayyana cewa wannan lamarin ya shafi injinan rarraba wuta guda takwas da ke samar da wuta a yankin tsakiyar Abuja, inda hakan ya haifar da rashin wutar sama da kashi 60 cikin dari na birnin.
Sai dai ta ce TCN ta tura tawagar injiniyoyi domin gyara wutar da sauri a yankunan da abin ya shafa.