Yadda sulhun tsagaita wuta tsakanin Hamas da Isra'ila ta kasance
Jiya Laraba ne da dare, 15 ga watan Rajab, 1446 AH, 15/01/2025, kasar Katar ta sanar da amincewar kungiyar Hamas game da sulhun tsagaita wuta da Isra'ila, ita kuma Amerika ta sanar da amincewar Isra'ila game da hakan. A yau ne Alhamis majalisar Isra'ila za ta zauna domin tattaunawa da amincewa da sulhun.
Yakin ya kwashe tsawon wata goma sha biyar, kwana 467. An rusa gine - ginen Gazzah kwata - kwata. An yi hasarar rayukan mutanen Gazzah fiye da dubu hamsin.
Idan ba wani abu ya shiga ba ana sa ran sulhun ya fara aiki ranar Lahadi in sha Allahu.
Sulhun mataki uku ne, amma yanzu a matakin farko ake. Matakin ya kunshi tsagaita wutar sati shida. A cikinsu za a saki fursunonin falasdinawa fiye da dubu, sannan Isra'ila za ta jaye sojojin ta daga cikin Gazza zuwa bakin boda. Ita kuma Hamas za ta saki fursunonin yahudawa talatin da uku, mata da tsoffi da marasa lafiya da matattu. Za a kuma ci gaba da shigar da abinci da sauran abubuwan bukata cikin Gazzah, mutane za su iya komawa garuruwansu da gidajen su ba tare da tsangwama ba, sannan za a iya fitar da masu munanan raunuka zuwa kasashen waje.
A mataki na biyu da na uku ana sa ran sakin fursunonin yahudawa gaba daya, da fursunonin falasdinawa masu yawan gaske, da ficewar sojojin Isra'ila gaba daya daga Gazzah, da kawo karshen yakin baki daya, da ci gaba da sake gina Gazzah.
@ Daily Nigerian Hausa