Yadda Wani Uba Yake Koyawa 'Ya'yansa Mata Sana'ar Faci Da Yake Yi

 Mahaifin wadannan yaran Bilkis da Khadija ya burge ni kwarai. Lokacin da na zanta da shi ce min ya yi "tunani na yi idan wani abu ya same ni yaya za su yi musamman ganin ya'ya mata Allah Ya azurta ni da su. Shi ya sa na koya musu sana'ata, ba abun da ba su iya ba, daga faci, sa iska da canza taya, kuma masana ne na Alqur'ani sosai, nan suke dawowa daga makaranta mu yi muraja'a tare idan aiki ya yi mana sauki, mu koma gida tare da yamma.

Uba ke nen da ke tunanin makomar ya'yanshi mata.

Akwai iyaye maza da mata dake tsaye kan lamuran ya'yansu duk da lalacewar zamani, ni dai kam ya burge ni sosai. 

Allah Ya ba mu ikon tarbiyantar da namu.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org