’Yan bindiga sun hallaka masu gaisuwar ta’aziyya kimanin 30 a ƙauyen Baure da ke Ƙaramar Hukumar Batsari a Jihar Katsina.
Masu gaisuwar ta’aziyya ciki har da ’yan banga, suna hanyarsu ta komawa gida ne ’yan ta’addan suka kai musu harin kwanton ɓauna inda nan take mutum 15 suka ce ga garinku nan.
Shaidu sun bayyana cewa mutanen da harin ya rutsa da su sun je ta’aziyyar ne daga ƙauyukan ƙananan hukumomin Safana da Kurfi da Charanchi da Kaita.
Aminiya