Zargin Damfara na Dala Biliyan 6: Fadar Shugaban Ƙasa ta ce Tinubu ya gode wa Buhari kan shaidar da ya bayar a kotun Paris
Fadar Shugaban Ƙasa a ranar Asabar ta tabbatar da rahoton da badakalar wutar manbila wanda tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana a gaban kotu a Paris kan zargin damfara na Dala Biliyan 6 da ya shafi aikin samar da wutar lantarki na Mambilla.
Sai dai fadar shugaban kasa ta ce Buhari ya halarci shari’ar a Paris ne da kansa ba tare da wani ya tilasta masa ba.
A cewar rahoton Peoples Gazette da ya danganta wani majiyar sirri, “An gurfanar da Buhari a gaban kotun a ranar Asabar bisa karya sharuddan yarjejeniyar samar da wutar lantarki da rarrabawa da aka bai wa kamfanin Sunrise Power and Transmission Company of Nigeria a zamanin tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo a 2003.”
Yayin da yake maida martani kan rahoton, kakakin Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga, ya musanta cewa Tinubu ya tilasta wa Buhari halartar shari’ar a Paris, amma ya tabbatar da cewa an yi wa Buhari tambayoyi a gaban kwamitin shari’ar.
“Duk da girmama sirrin wannan shari’ar, muna so mu bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai tilasta wa kowa bayar da shaida ko kaurace wa bayar da shaida kan Najeriya ba,” in ji Onanuga a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, jim kaɗan bayan rahoton Gazette ya bazu a kafofin sada zumunta.
“Wannan shari’ar da ake gudanarwa a sirrance bai kamata ta fito fili ba har sai lokacin da kwamitin shari’ar ƙasa da ƙasa ya yanke hukunci,” in ji shi.
Akasin al’adar da aka saba gani inda tsoffin shugabannin Najeriya ke watsi da gayyatar kotu, an yi wa Buhari tambayoyi na tsawon sa’o’i a kotun ƙetare.
A cikin rahoton musamman da ta fitar, Gazette ta ruwaito cewa majiyoyi sun tabbatar da cewa, “Shugaba Bola Tinubu ne ya amince a gurfanar da magabacinsa a gaban kotun ƙetare.”
Wani babban jami’i a gwamnatin Tinubu ya ce Buhari bai yi niyyar bayar da shaida kan lamarin ba. “Sai dai Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, ya ziyarce shi a gidansa da ke Daura makon da ya gabata domin tilasta masa zuwa Paris. Ministan ya fayyace wa shugaban cewa dole ne ya bayyana a Paris,” in ji majiyar, wadda ta nemi a sakaya sunanta.
ATP Hausa