Atiku ya yaba wa Adeleke bisa gudanar da zaɓen ƙananan hikimomi duk da gargaɗi daga gwamnatin taraiya da rundunar ƴansanda
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yabawa gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, kan yadda ya gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa babban Lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Lateef Fagbemi da kuma rundunar ‘yan sandan Najeriya, sun bukaci gwamnan da ya dakatar da zaben bisa ga umarnin kotu da kuma sahihan bayanan sirri na yiwuwar tashin hankali a jihar.
Sai dai gwamnatin jihar Osun din ta yi watsi da shawarar tsaro da rundunar sandan Najeriya ta bayar na dakatar da zaben.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a, Kolapo Alimi ya sanyawa hannu a jiya Juma’a, gwamnatin jihar ta bayyana cewa dalilan yin watsi da shawarar sun ta’allaka ne da bin doka da oda da kuma kyamar bangaranci na ‘yan sanda.
Sai dai a cikin wani sakon da ya wallafa a shafin sa na X ranar Asabar, Atiku ya yi kira da a gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.
Ya kuma bukaci hukumomin tsaro da jami’an zabe da su gudanar da ayyukansu tare da kare al’umma.