Bakar fata ƴar asalin Najeriya, Amanda Azubuike, ta samu ƙarin matsayi zuwa Birgediya-Janar a rundunar sojin Amurka, inda ta zamto mace ƴar Najeriya ta farko da ta samu wannan matsayi.
An haifi Amanda Azubuike a birnin Landan na kasar Birtaniya bayan da mahaifin ta dan kabilar Igbo da kuma mahaifiyar ta ƴar kasar Zimbabwe su ka yi aure.
Mahaifinta ya bar Najeriya tun yana karami, inda ya karanci aikin lauya a kasar Burtaniya, inda ya hadu da mahaifiyarta, matashiya dalibar aikin jinya.
Tafiyar ta zuwa aikin soja ta fara ne lokacin da mahaifiyarta ta yi ƙaura zuwa Amurka tare da su biyun, Amanda, da 'yar uwarta bayan aurenta ya mutu. Ta samu shaidar zama ɗan Amurka a watan Afrilun 1989.
Azubuike ta kammala karatu na digiri na farko a Jami'ar Central Arkansas a fannin Sadarwa a cikin Disamba 1993 kuma ta shiga aikin soja a 1994 a matsayin direban jirgin sama bayan ta kammala karatun Babbar Jami'in Harkokin Jirgin Sama.
Bayan shekara guda, Azubuike ta kammala karatun koyon tukin jirgin sama a matsayin matukin jirgi na UH-1 kuma ta fara aikin soja a filin jirgin saman Hunter Army da ke Jojiya a matsayin shugabar runduna tare da Bataliya ta 924 na Koyon Tukin Jirgin Sama.