Duk da gargaɗi daga gwamnatin tarayya da rundunar ƴansanda, Adeleke ya gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a Osun

 Duk da gargadin da Gwamnatin Tarayya da Rundunar ‘Yansanda ta Najeriya su ka yi, zaben kananan hukumomi a jihar Osun na gudana a halin yanzu.

Gwamna Ademola Adeleke ya kada kuri’arsa a rumfar Zabe ta 9, Sagba Abogunde, Gundumar 2, Karamar Hukumar Ede Arewa, da misalin karfe 7:56 na safe.

A cewar NAN, gwamnan ya isa rumfar zaben tare da magoya bayansa da wasu ‘yan jam’iyyar PDP.

Adeleke ya yaba wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Osun (OSSIEC) kan yadda aka gudanar da zaben cikin lumana.

Gwamnan ya shawarci mazauna jihar da su fito su kada kuri’arsu ba tare da tsoro ko fargaba ba, yana kuma kira ga masu ruwa da tsaki da masu kada kuri’a da su nisanci tashin hankali kafin da bayan zaben.


Daily Nigeria Hausa 

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org