El-Rufai yace shi ban iya munafurci ba
Tsohon gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai, ya ce shi ba irin 'yansiyasar nan ba ne da ke munafurci da yaudara da karya ba, yana mai kwatanta 'yansiyasar da ke haka da 'yan fim din Najeriya.
El-Rufai ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da magana kan wani da ya yi rubutu a shafin X, Ira Habib inda ya koda shi bayan da ya ce ya karanta littafinsa ‘Accidental Public Servant,’
Habib ya rubuta cewa,''...lalle ba dansiyasar da zai so ya yi aiki da El-Rufai a majalisar ministocinsa sai dai in har da gaske yake yana son ya raya kasarsa nan. Bai iya munafurci ba.'' Kamar yadda mutumin ya rubuta a shafinsa na X.
A kan hakan ne El-Rufain ya jaddada maganar da Habib din ya rubuta cewa bai iya yaudara da karya ba - yana mai kwatanta 'yansiyasar da ke haka da 'yan fim din Najeriya na Nollywood.
Tsohon gwamnan na Kaduna ya bayyana hakan ne kuwa 'yan kwanaki bayan da aka ruwaito shi yana cewa idan da yana cikin gwamnatin Tinubu ba zai sauya matsayinsa ba a kan yadda yake faden gaskiya a kan gwamnatin ba.
BBC HAUSA