IBB a Cikin Littafinsa Ya Bayyana Yadda Murtala Muhammed Ya Zama Shugaban Kasa da Kuma Ranar da Aka Kashe Shi

 A cikin littafinsa, IBB ya bayyana cewa farkon mulkin Murtala Muhammed ya zo da sallamar jami’an gwamnati da ba a taba ganin irin ta ba a tarihin Najeriya.

Ya rubuta: “Daya daga cikin zarge-zargen da aka yi wa Janar Gowon (wanda daga baya muka fahimta bai dace ba) shi ne cewa yana tafiyar da mulki kamar mutum daya ne kawai ke da iko! Saboda haka, mu ‘yan matasa a cikin manyan hafsoshi da muka taka rawa a juyin mulkin, mun yanke shawarar cewa dole ne sabuwar gwamnatin bayan Gowon ta kasance mai tafiya a kan tsari na hadin gwiwa. Mun yanke hukunci cewa Brigadiya Murtala Muhammed ne zai zama Shugaban Kasa, amma manufarmu ita ce a tabbatar da cewa yana tafiyar da mulki a matsayin shugaba ne kawai amma ba wanda zai yi mulkin mallaka ba. Don haka, sai aka nemi Muhammed da ya yarda da wannan tsari, amma mun san cewa zaiyi  wahala a shawo kansa.”

“A cikin taron da aka yi da shi tare da Olusegun Obasanjo da Theophilus Danjuma, Murtala ya yi watsi da duk wani shirin da zai hana shi cikakken iko a matsayin Shugaban Kasa. A rana ta gaba, ya yi gaggawar sallamar manyan jami’ai da dama, ciki har da Mataimakin Shugaban Kasa, Vice-Admiral Joseph Wey, da manyan hafsoshin sojoji kamar Hassan Katsina, David Ejoor, Nelson Soroh, da Emmanuel Ikwue. Haka kuma, ya tsige babban sifeton ‘yan sanda Alhaji Kam Salem da mataimakinsa T. A. Fagbola.”

“Wadannan sauye-sauyen sun hada da sabbin nade-nade da aka yi. Brigadiya Olusegun Obasanjo ya zama Mataimakin Shugaban Kasa, yayin da Brigadiya Theophilus Danjuma ya zama Shugaban Hafsoshin Sojoji. Haka nan, an nada Alhaji Mohammed Dikko Yusuf a matsayin Sifeton ‘Yan Sanda, Colonel John Yisa-Doko ya zama Shugaban Hafsoshin Sojin Sama, sai Commodore Michael Adelanwa da aka nada Shugaban Hafsoshin Sojin Ruwa.”

Juyin Mulkin Dimka da Kisan Murtala Muhammed

IBB ya bayyana yadda rana ta Juma’a 13 ga Fabrairu, 1976, ta kasance a gare shi. Ya ce da safiyar ranar, maimakon bin hanyar Osborne Road kamar yadda ya saba, ya zabi wata hanya daban. Daga baya aka gano cewa sojojin Dimka sun kitsa masa tarko a Osborne Road don su kashe shi, amma ya kubuta ba tare da sanin hakan ba.

A wannan rana ce sojojin da suka jagoranci juyin mulki suka yi kwanton ɓauna suka harbe Murtala Muhammed tare da direbansa da mai tsaronsa a lokacin da yake kan hanyarsa zuwa aiki. Sojojin sun yi amfani da bindigu sosai har sai da suka tabbatar da cewa ya mutu a wurin.

IBB ya bayyana cewa da zarar ya isa Hedikwatar Sojoji, aka gaya masa cewa juyin mulki ne ake yi. Sai aka umurce shi da ya tafi gidan rediyo don dakile Dimka. Lokacin da ya isa gidan rediyon, Dimka ya yi kokarin hana shi shiga, har ya yi barazanar harbe shi, amma IBB ya yi masa magana har ya shawo kansa.

A lokacin da suka yi magana, Dimka ya bayyana cewa ba su yarda da IBB ba, kuma yana daya daga cikin mutanen da aka tsara za a kashe. Dimka ya nemi IBB ya shiga juyin mulkin, amma daga bayansa ya fara neman amincewa da kariya. IBB ya bashi shawara ya mika kansa, amma Dimka ya ki amincewa.

Bayan IBB ya koma hedikwatar sojoji, aka umarce shi ya koma gidan rediyo don fatattakar Dimka. Da suka koma tare da sojojin da suka tsaya ga gwamnati, aka yi artabu da sojojin Dimka, aka kashe wasu daga cikinsu ciki har da mataimakin Dimka, amma Dimka ya tsere ba tare da an kama shi a wancan lokaci ba.

A ranar 14 ga Fabrairu, 1976, gwamnatin tarayya ta sanar da mutuwar Murtala Muhammed tare da ayyana kwanaki bakwai na zaman makoki. A wannan rana ne aka binne shi a Kano a gaban dubban jama’a da manyan jami’an gwamnati, ciki har da Janar Bisalla wanda daga baya aka same shi da hannu a juyin mulkin.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org