Jami’an Tsaro Za Su Dauki Mataki Kan ’Yan Siyasa Masu Tunzura Rikici Akan Tinubu — Matawalle.

 Ministan Harkokin Tsaro na Ƙasa, Dr. Bello Muhammed Matawalle, ya gargadi ’yan siyasa masu tunzura rikici da maganganun da ke barazana ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu cewa jami’an tsaro za su sanya ido kuma su dauki mataki a kansu.

Matawalle ya bayyana haka ne yayin da yake mayar da martani kan wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, inda tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, ake jin yana cewa dole ne ’yan siyasa su “sata, su raunata, su kashe” domin su ci gaba da riƙe mulki.

Ministan ya soki wannan furuci da ƙarfi, yana mai cewa maganganun na Amaechi ba su da hankali kuma suna da niyyar tayar da zaune tsaye a ƙasar.

Ya ce, “Amaechi da sauran waɗanda ke tunanin za su iya amfani da matasa don haifar da rikici ya kamata su sake nazarin irin wannan dabi’a. Wannan gwamnati ba za ta yi shiru tana kallo ba yayin da kowa ke ƙoƙarin lalata zaman lafiya da tsaron Najeriya,” in ji shi.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Watsa Labarai na Ma’aikatar Tsaro, Henshaw Ogubike, ya fitar, Ministan ya bayyana cewa maganganun Amaechi ba wai kawai suna cin mutuncin hankalin ’yan Najeriya ba ne, har ma suna ƙoƙarin tunzura matasa da tayar da zaune tsaye wanda zai iya lalata zaman lafiya da tsaron ƙasa.

Ya ƙara da cewa, “Abin takaici ne kuma haɗari ga tsohon mai rike da mukamin gwamnati ya yi irin waɗannan kalamai masu tunzura rikici. A daidai lokacin da gwamnati ke aiki tukuru don ƙarfafa haɗin kan ƙasa da zaman lafiya, babu wani shugaba na gari da zai riƙa hura wutar rikici da rashin zaman lafiya.”

Matawalle ya ja kunnen ’yan siyasa da su guji yaudarar matasa da labaran ƙarya da ke tunzura su zuwa tashin hankali, yana mai jaddada cewa Najeriya ƙasa ce da ke bin doka, ba daji ba ne da ake karɓar mulki da ƙarfi da mugunta.

“Ina so in bayyana karara: jami’an tsaro suna cikin shiri. Duk wanda aka kama da laifin tunzura rikici ko ƙoƙarin tayar da hankulan jama’a zai fuskanci cikakken hukuncin doka. Ba za mu lamunci kowane irin furuci ko aikin da zai tunzura mutane da yaɗa rashin doka da oda ba,” in ji shi.

Ministan ya bayyana cewa, akasin ikirarin Amaechi, mulki ana samun sa ne ta hanyar dimokuraɗiyya ba ta hanyar firgita mutane, tashin hankali ko rashin bin doka ba.

Ya jaddada cewa gwamnatin Shugaba Tinubu za ta ci gaba da bin hanyoyin tabbatar da zaman lafiya, mutunta ƙa’idojin dimokuraɗiyya, da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org