Obasanjo ya koka kan raguwar karatun litattafai ga matasa
Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana damuwarsa kan yadda ake kara samun tabarbarewar karatun littattafai ga matasan Najeriya, ya na mai cewa hakan na iya lalata tarihin adabin kasar nan.
Ya bayyana haka ne a jawabinsa a taron ‘Karatun Marubuta’ na kungiyar Marubuta ta Najeriya, ANA, a jiya Asabar a Abuja.
A cewar Obasanjo, Najeriya ta kwashe shekaru tana baje kolin haziƙan marubuta adabi da ake buga misali da ayyukansu a duniya, don haka akwai bukatar a samar da matasa marubuta domin dinke barakar da ake samu a fagen adabi.
Ya ce karatu shi ne tabbataccen hanyar zama marubuci, amma da yawa daga cikin matasa a wannan zamani ba sa son karatu duk da sauƙin samun bayanai da ƙafar yanar gizo ke bayarwa.
Obasanjo ya koka da cewa idan ba a magance ba, yanayin ba zai shafi tarihin adabin Najeriya kadai ba, zai haifar da samuwar shugabanni marasa wayewa da gazawa a nan gaba.