Babu hawan Sallah a Kano, -Hukumar 'Yansanda jihar Kano.

 'Gamayyar jami'an tsaro a jihar Kano, sun dakatar da daukacin hawan sallah da aka saba gudanarwa a kasar kano.

Kakakin rundunar 'yansandan na jihar Kano, Abdullahi kiyawa ne ya wallafa haka a shafinsa na Fesbuk, inda ya ce babu hawan sallah a Kano, Jaridar Taskar Labarai ta ruwaito.

Hakan na nufin jami'an tsaron sun dakatar da shi kansa sarki Sanusi Lamido Sanusi daga hawan Sallahn.

Da ma dai tuni Sarki Alhaji Aminu Ado Bayero ya sanar cewar ba zai yi hawan Sallar ba saboda kiranye-kiranye masu fada aji suka yi don samu zaman lafiya a jihar.

Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org