Matasa sun wawashe abincin Ramadan da Seyi Tinubu zai raba a jihar Gombe

Wasu fusatattun matasa sun dakawa abincin da ɗan gidan shugaban kasa, Seyi Tinubu ya je zai raba a jihar Gombe, kamar yadda ya ke a sauran jihohin Arewa da ya ke ta ziyar ta.

Daily Trust ta rawaito cewa a wani faifen bidiyo, an ga matasan sun dirar wa motar dakon abincin, inda su ka riƙa diba suna yin nasu waje.

An hango matasan da suke kan motar na jefawa wadanda su ke kasa kunshin abincin da ya kun shi shinkafa, sukari, man girki da taliya.

Trust ta rawaito cewa mota biyu aka baiwa Gombe kason ta na kayan abincin da su ka kunshi katan 3,500 na abincin, inda bayan an raba mota daya ba gare da hatsaniya ba, dayar kima sai matasan su ka daka mata wawa.

Daily Trust ta rawaito cewa ba ta samu jin ta bakin jam'iyyar APC ba a jihar.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org