2027: Dalilin da ya da sa mahaifi na ba zai yi Atiku ba - Ɗan Gwamnan Bauchi

 


Shamsudeen Bala Mohammed, dan gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana cewa zai yi wuya mahaifinsa ya goyi bayan takarar shugaban kasa na tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.

Dan gwamnan ya bayyana hakan ne a wani sakon da ya wallafa a shafin sa na X @shamsudeen_bala a jiya Juma’a yayin da ya ke mayar da martani ga wani sakon tambaya da wani mabiyinsa  a shafin ya aike masa, wanda ya nuna sha’awar sa na ganin Atiku da Mohammed sun hada kai domin ceto jam’iyyar PDP.

Ya zargi tsohon mataimakin shugaban kasar da yin adawa ga sake tsayawa takarar mahaifinsa tare da zuga manya a Bauchi su kalubalance shi 

"Gaskiya, zai yi wahala. Domin ko ya yi nasara, babu abin da zai yi mana illa ga yi amfani da mu ya cimma bukatar sa.

“Sannan kuma, bai bamu goyon baya ba a 2023 ba. Ya goyi bayan Air Marshal [Dan takarar APC].

“Ya kuma zuga manyan Bauchi domin su yaƙe mu har sai da muka tsira da kyar, kuma yana mutunta mu da kima.

"Ya ci gaba da nuna mana cewa ba mu cancanci ya tattauna da mu ba," in ji Shamsudeen.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org