Ɓata gari sun tilasta wa mata mai ciki haihuwa sannan suka sace jaririnta
Lamarin Ban Mamaki: Ɓata gari sun tilasta wa mata mai ciki haihuwa sannan suka sace jaririnta Wani lamari mai tayar da hankali ya faru, inda wasu bata-gari suka tilasta wa wata mata mai juna biyu yin haihuwa da wuri sannan suka yi awon gaba da jaririn da ta haifa. Rahotanni daga yankin sun bayyana cewa matar,
wadda ta kusa haihuwa bisa ga kwanakin da likitoci suka kayyade (EDD), na kan hanyarta ta komawa gida ne lokacin da wasu suka tareta tare da kaita wani wuri da ba ta iya ganewa ko gane inda take ba.
A cewar matar, bayan da suka isa wurin sai wani mutum da ya bayyana kamar jami'in lafiya ya ba ta wasu kwayoyi, wanda nan da nan suka jawo ta fara nakuda, inda ta haifi jariri a nan take. Sun shaida mata cewa jaririn kawai suke bukata, ba da ita ba – hakan yasa ba su cutar da ita ta wani hanya ba. Wasu makwabta sun ce tun tuni matar ta rika kuka da cewa tana jin kamar ana bibiyarta, kuma akwai alamun wani abu na faruwa. Mijin matar ya tabbatar da faruwar lamarin,
kuma tuni ya shigar da kuka a ofishin ‘yan sanda da ke unguwar Rijiyar Zaki domin a fara bincike cikin gaggawa. Wannan lamari ya bar jama'a cikin firgici da kuma tambayoyi da dama: Wa ke da hannu a wannan aika-aika? Me yasa aka sace jaririn? Kuma ta yaya za a hana faruwar hakan a gaba?