Rahar da Buhari ya yi wa Atiku ta ‘Sannu da gwagwarmaya’ a Kaduna ta bar baya da ƙura
Anas DansalmabyAnas Dansalma April 12, 2025
Rahar da Buhari ya yi wa Atiku ta ‘Sannu da gwagwarmaya’ a Kaduna ta bar baya da ƙura
A ranar Juma’a ce tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubukar ya kai ziyara ga tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, a gidansa da ke Kuduna.
Atiku ya kai wannan ziyara ce tare da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da Aminu Tambuwal da Gabriel Suswam, da tsohon ministan sadarwa da tattalin arziƙi na zamani, Isa Pantami da sauransu waɗanda suka kai wa tsohon shugaban ƙasa ziyarar ba zata.
A wani bidiyo da ke yawo a kafofin sada zumunta, an hangi tsohon shugaban ƙasar da Atiku suna raha wanda a nan ne aka ji Buhari na yaba wa Tinubu kan ƙoƙarin da yake yi a siyasance.
Wannan raha dai sun yi ta ne cikin harshen Hausa.
“Salamun alaikum, ” Ina yi muku maraba sannau da wannan gwagwarmaya,” in Buhari cikin raha.
Buhari ya zaga inda ya gaisa da kowa da aka zo tare da shi a yayin da El-Rufai ya durkusa har dab da ƙasa cikin salon da ya saba gaishe da Buhari.
Babban abin da ya ja hankali kuma ya sa mutane mamaki shi ne yaba wa Atiku da Buharin ya yi kan gwagwarmayar da yake yi,
sai dai bai ƙarin haske kan wacce gwagwarmaya yake nufi ba. Sai dai a fili yake cewa yana nufin gwagwarmayar da yaƙi da jam’iyya mai mulki ta APC.
Har izuwa yanzu dai ba a faɗi dalilin kai wannan ziyara, sai dai daga baya Atikun ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa wannan ziyara ce ta gaisuwar sallah suka kai wa Buharin.
“A matsayina na Wazirin Adamawa, da sallah na zauna ne an yi bikin sallaha tare da Lamido Fombina.”
“A yau kuma, na samu damar kai ziyarar bayan sallah ga shugaba Buhari wanda ya yi mulki daga shekarar 2015-2023. Kuma mun ji daɗin ziyarar.”
“Kamar kullum, mun yi wasa dariya kamar cikina zai yi ciwo saboda irin barkwancin Buhari.
Bayan ziyarar ce kuma El-Rufai ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa sun yi sallar juma’a tare da tsohon shugaban a masallacin Yahaya Road Mosque da kuma cin abinci a gidan Buhari.
Tsohon gwamnan Kaduna ya ce wannan ziyara ba ta shafi siyasa ba, ziyara ce ta nuna ‘yan uwantaka ga tsohon shugaban.
“Bai kamata hamayyarmu ta hana mu bacci ba. Ba batu ne na siyasa ba, batu ne na haɗin kai da ‘yan uwantaka tun da dukkaninmu ba wani mai muƙamin siyasa. Don haka, mun yi sallah, mun ci abinci da jagoranmu,” in ji El-Rufai.
Hakazalika, Dele Momodu, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa, “wannan ziyara ce da ta shafi nuna girmamawa ga shugaban da tattaunawa da girmama juna ba tare da la’akari da siyasa ba.
Sauran waɗanda suka yi wa Atiku rakiya sun haɗa da tsohon gwamnan Adamawa, Mohammed Bindow, da tsohon gwamnan Imo, Achike Udenwa da tsohon gwamnan Benuwai, Gabriel Suswan.
Sauran sun haɗa da: sanata Idris Umar da Mohammed Kumalia da Yahaya Abubakar da Musa Halilu daDujiman Adamawa da Salisu Makarfi.
Atiku wanda shi ne jagoran jam’iyyar Adawa ta PDP wa gaza kai bantansa a zaɓen da ya kara da Buhari a 2019. Sannan ya faɗi zaɓe a karawar da ya yi da shugaba Tinubu mai ci a zaɓen 2023.
Buhari dai ya riƙe shugabancin Najeriya ne daga shekarar 2015 zuwa 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar APC wacce ita ce mai mulkin ƙasa a yanzu.
ATF Hausa