Tsohon kyaftin kuma kocin Super Eagles, Christian Chukwu ya mutu
Tsohon kyaftin kuma kocin din Super Eagles, Christian Chukwu ya mutu yana da shekaru 74 a duniya.
Shahararren dan wasan kwallon kafar ya rasu da safiyar yau Asabar, duk da cewa har yanzu ba a san sanadiyyar mutuwar ta sa ba.
Abokin taka ledar sa, Olusegun Odegbami ne ya tabbatar wa gidan talabijin na Channels TV wannan labarin mutuwar Chukwu.
Odegbami, wanda ya lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka a shekarar 1980 tare da Chukwu, ya ce: “Na samu labarin cewa tsakanin karfe 9:00 zuwa 10:00 na safiyar yau, ‘Shugaban’ Christian Chukwu, MFR, abokina kuma abokin wasana, daya daga cikin manyan ‘yan wasan kwallon kafa a tarihin Najeriya, ya mutu.
"Babuje, Emmanuel Okala, MON, ya ba ni labari mai ban tausayi 'yan mintoci kaɗan da suka wuce, Allah ya sa 'Onyim' ya sami zaman lafiya da Mahaliccinmu a cikin Sama ya kuma ta'azantar da danginsa," in ji Odegbami.
An haife Chukwu a ranar 4 ga Janairu, 1951, inda ya fara rayuwar ƙwallon ƙafar da da ƙungiyar Rangers, inda ya yi musu kyaftin a fagen wasan kwallon kafa na cikin gida, kuma ya jagoranci ƙungiyar zuwa daukakar kogin nahiyar ta hanyar lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka ta kungiyoyin ƙwallon ƙafa da aka yi a 1977.
Shi ne kyaftin din Najeriya na farko da ya dauki kofin gasar cin kofin kasashen Afirka bayan da suka doke Algeria da ci 3-0 a wasan karshe na gasar 1980 a Legas.